Shadiun sun ce ‘Yansanda basu yi wata wata ba wajen tarwatsa zanga zangar da aka shirya a Alkahira, da Ismaliya, da Alexandria da kuma Giza. Tunda farko hukumomin kasar sun yi kashedin cewa basu amince da duk wata zanga zanga daga ‘yan kungiyar ba, bayanda masu iko a kasar suka ayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta’adda cikin watan jiya.
Ma’aikatar kiwon lafiya kasar tace biyar daga cikin wadanda rikicin ya rutsa da su sun gamu da ajalinsu ne a birnin Alkahira, sai dai ma’aikatar batayi bayani ko wadnasda aka skashen ‘Yansanda ne ko masu zanga zanga ko kuma ‘yan kallo ne.
Gwamnatin kasar wacce take samun goyon bayan sojoji, da suka kifar da gwamnatin Mr. Morsi cikin watan Yulin bara, suna amfani da ayyana kungiyar ta Muslim Brotherhood a matsayin ta “Yan ta’adda” wajen tsare daruruwan magoya bayan kungiyar. Wasu dubbai ciki harda shugabannin kungfiyar ana daure dasu na wattani.