Ba Zan Iya Ci Gaba Da Shiga Tsakani Ba Wajen Neman A Sako Sauran Fasinjojin Da Aka Sace – Malam Tukur Mamu

Wani jirgin kasan Najeriya

Bayanai sun yi nuni da cewa har yanzu akwai sauran mutum 44 a hannun 'yan bindigar dajin.

Sa'o'i kadan da sakin karin mutane bakwai daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da 'yan-bindiga su ka sace, shugaban kamfanin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu wanda ya jagoranci sakin mutanen, ya ce ba zai kara shiga cikin maganar ba duk da ya ke ya tabbatar da cewa har yanzu akwai mutane 44 a hannun 'yan-bindigan.

A ranar Asabar ne dai labarin sakin mutane 7 cikin ragowar 51 dake hannun 'yan-bindigan da su ka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna, ya bazu ko ina.

Malam Mamu ya ce ba zai kara tsoma baki game da maganar fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kadunan da ke hannun 'yan-bindigan ba saboda rayuwarsa ta na cikin hadari.

Sai dai duk da haka ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa sauran mutane 44 da ke hannun 'yan-bindigan su nan a raye.

Wadanda aka saki a ranar dai su ne Sadiq Ango Abdullahi, wanda da ne ga shugaban kungiyar dattawan Arewachin Najeriya da Muhammad Dayyabu Paki, tsohon shugaban karamar hukumar Ikara kuma shugaban wata hukuma a jihar Kaduna, sai Bosede Olurotimi da Abubakar Zubairu da Alhassan Sule da Aliyu Usman da kuma Muhammad Abuzar Afzal, wanda dan asalin Pakistan ne.

Malam Sani Lawal, daya ne daga cikin masu magana da yawun 'yan'uwan wadanda aka sacen kuma ya ce yanzu duk mutane bakwan da aka saki suna gida tare da iyalansu.

Malam Lawal ya ce mutane bakwan da aka sako duk sun rame kuma dun yi baki amma dai suna cikin hankalinsu don har sun kawo sakon gaisuwa daga sauran wadanda su ka rage a hannun 'yan-bindigan.

Tun ranar 28 ga watan Maris na wannan shekara ne 'yan-bindiga su ka datse jirgin kasan Abuja-Kaduna inda su ka sace mutane sama da sittin (60) sannan su ka kashe wasu kuma su ka bar wasu da raunika amma daga bisa su saki mutane 11 naya sakin wani dattijon da su ka ce saboda bashi da lafiya ne.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Zan Iya Ci Gaba Da Shiga Tsakani Ba Wajen Neman A Sako Sauran Fasinjoji Da Aka Sace – Malam Tukur Mamu - 3'52"