ABUJA, NIGERIA - Rahotanni sun bayyana cewa an sako Mutanen ne bayan doguwar tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan bindigar, abinda ya sa suka sako mata shida da maza biyar ranar Asabar.
An ce mai jaridar Desert Herald Tukur Mamu, shi ne wanda ya shiga tsakanin gwamnati da ‘yan ta'addan a kokarin ganin an sako Mutanen.
Jaridar Daily trust ta bayyana sunayen Mutanen da aka sako: Amina Ba’aba Mohammed, Amina Jibril, Danjuma Sa’idu, Gaius Gambo, Rashida Yusuf Busari, Hannah Ajewole, Hassan Aliyu, Jessey John, Najib Mohammed, Dahiru, da Peace A. Boy.
Mamu ya bayyana cewa dole ne a godewa shugaba Muhammadu Buhari, da Hafsan hafsoshin sojan Najeriya, da ma sauran shugabannin tsaro saboda gudummuwar da suka bada wajen sako Mutanen.
Hakazalika ya ce babban malamin Islama da ke Kaduna Sheikh Ahmad Gumi, shi ma ya taka rawa ta bayan fage.
An kai mutanen da aka sako wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja don jinyar.
Gwamnatin Najeriya dai ta kasa dawo da jigilar mutane ta jirgin kasa saboda kasancewar wadanda aka sace na hannun 'yan bindigar.
Harin 'yan bindigar ya auku ne a ranar 28 ga watan Maris na 2022 a dajin Dutse da ke karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna. Mutane sama da ashirin suka rasa rayukansu wasu da yawa kuma suka jikkata.
Marubuci Alhassan A. Bala