Tun daga ranar da aka kai harin kan jirginkasar, hukumomi su ka dakatar da zirga-zirgar jiragen, lamarin da ya jefa 'yan-kasuwa da masu sana'oin karfi a filin jirgin kasan cikin mawuyacin
hali.
Tashar jirgin kasan da ke Rigasa a karamar hukumar Igabin jahar Kaduna da ake samun turmutsimutsin motoci da mutane lokacin da jirgi ke aiki, yanzu ta zama wayam ba kowa sai masu zaman jiran tsammani.
A hirarshi da Muryar Amurka, shugaban kungiyar 'yan-kasuwan filin mai barin gado Malam Yakubu Abubakar Kubaraci ya bayyana cewa, galibin wadanda su ke sana'a a tashar sun kauracewa wurin sabili da rashin kasuwa. Bisa ga cewarshi, su da su ke zuwa suna zuwa ne sabili da sabo da kuma rashin wata sana'a, ya kuma yi kira ga hukumomi su nemi hanyar samar da tsaro domin ci gaba da sufurin jirgin kasar da kuma maido da harkokin kasuwanci a tashar ta Rigasa.
Masu sharhi akan al'amurran yau da kullum, irin su Farfesa Khalifa Dikwa dai na ganin dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa, wata matsala ce mai zaman kanta game da tsaro.
Har yanzu dai akwai mutanen da 'yan-bindigan su ka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna da dama a hannun su duk da sa'ar sakin wasu daidaiku da kuma wasu 11 a makon da ya gabata.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti: