A Laraban nan ne dai labarin sakin mutanen da 'yan-bindiga su ka kama su ka dunga yawo a kafafen sada zumunta har ma wasu na cewa duk mutanen da aka kama sun koma gida, sai dai daya daga cikin 'yan'uwan wadanda aka sacen ya ce labarin ba shi da tushen gaskiya.
Wannan dai ba shine karo na farko da labarun kanzon kurege ke yawa game da sakin mutanen da 'yan-bindiga su ka kama ba, abun da ya sa masani kan harkokin tsaro, Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce salo ne na saka siyasa aka fito da shi.
Mai magana da yawun hukumar jiragen kasan Najeriya malam Mahmud Yakubu ya shedawa Muryar Amurka cewa, ba su san komai game da sakin wadanda aka kama ba sai dai shi Malam Sani Lawal din da 'yan-uwan shi biyu ke hannun 'yan-bindigan ya ce kwanaki saba'in da biyu (72) da kama 'yan'uwan su, suna cikin wani hali.
Har yanzu dai babu wani labari game da cigaba da aikin jirgin kasan Abuja-Kaduna tun bayan yunkurin cigaba da aikin da ya yi karo da zanga-zangar 'yan-uwan wadanda aka sace a Kaduna.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: