KADUNA, NIGERIA - Labarin harbin daya daga cikin wadanda 'yan-bindigan su ka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna mai suna Mohammed Al'Amin dai shi ne dalilin kiran taron manema labarai da 'yan uwan su ka yi, inda Malam Sani Lawal ya yi magana da yawun sauran 'yan'uwan wadanda aka sacen.
Wasu daga cikin 'yan'uwan wadanda aka sacen dai ba su iya magana ba saboda su na ta kuka sai wasu daga cikinsu ne dole suka bayyana halin kunci da su ke ciki.
Malam Sani Lawal ya ce mutane 50 ne yanzu a hannun 'yan-bindigan, ya ce kuma dukan su ne gwamnati ta tabbatar da an sako su idan kuma ba haka ba ranar da kwanaki dari za su cika, za su yi zanga-zanga a Kaduna da Abuja.
Tun a jiya Alhamis dai hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Genaral Lucky Irabor ya shaidawa gidan talabijin na Arise cewa gwamnati da jami'an tsaro na kokarin ganin an sako wadannan mutane, kuma nan ba da dadewa ba za su dawo gida.
Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara: