A yau Alhamis 9 ga watan Nuwambar nan ne kungiyoyin na NLC da TUC suka gudanar da zanga-zangar da suka bayyana a matsayin wani matakin da suka dauka biyo bayan afkawa shugaban kungiyar NLC Joe Ajaero a jihar Imo kamar yadda sakataren tsare-tsaren kungiyar NLC, Kwamared Nasir Kabir ya shaida mana.
Tuni dai wasu ‘yan Najeriya suka yi ta bayyana yanayin da matakin na kungiyoyin kwadagon ya sanya su a ciki, wasu sun gagara zuwa wajen aikin su a yau din.
A nasa bangare, masanin tattalin arziki, Mal. Kasim Garba Kurfi, ya ce zanga-zangar tsaida abubuwa cir musamman a filin tashi da saukar jiragen saman kasa-da-kasa zai shafi tattalin arzikin Najeriya ya kuma tsorata masu zuba jari shigowa cikin kasar.
Lamarin nan dai ya samo asali ne daga jihar Imo inda aka sami taho-mu-gama tsakanin gwamnatin Jihar Imo da taron mambobin kungiyar NLC da Joe Ajaero ya jagoranta.
Idan ana iya tunawa, daga watan Mayun da shugaba Tinubu ya karbi rantsuwar kama aiki da cire tallafin man fetur, kungiyoyin kwadago sun yi zanga-zangar lumana don mika koken yan Najeriya ga gwamnati kuma akwai yiyuwar a sake shiga wani yajin aikin nan bada jimawa ba idan gwamnati bata cika alkawurranta a yarjejeniyar da aka cimma na rage radadin da yan kasa ke ciki sakamakon cire tallafin man feutr a watan Ajiya.
Ko a kasashen da suka ci gaba ma ana samun zanga-zangar nuna rashin amincewa ko kin jinin gwamnatin da ake zargi da aikata laifuka.
Your browser doesn’t support HTML5
Saurari rahoton: