Kungiyoyin dai sun yi ta tursasa wa shugaban kasa Bola Tinubu kan ya janye matakin da ya dauka a watan Mayu na soke tallafin man fetur wanda ya yi sanadiyar kudin mai ya yi kasa ciki shekaru da dama da suka gabata amma kuma ya daura wa kudaden gwamnati nauyi.
Farashin ya yi tashin gwauron zabo, ciki har da farashin abinci, sufuri da wutar lantarki, yayin da galibin ‘yan kasuwa da magidanta ke dogaro da injinan janareta na man fetur wajen samun wutar lantarki.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya da manyan kungiyoyin kwadago sun ce za su fara yajin aikin a ranar 3 ga watan Oktoba.
"Zai zama rufe komai da komai baki daya... har sai gwamnati ta biya bukatun ma'aikatan Najeriya, da ma talakawan Najeriya," in ji shugabannin kungiyar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa.
"Gwamnatin tarayya ta ki yin aiki mai ma'ana tare da cimma yarjejeniya da kungiyoyin kwadago kan muhimman batutuwan da suka shafi illar rashin sahihancin hauhawar farashin man fetur wanda ya sanya ma'aikata da talakawan Najeriya cikin kunci."
Gwamnati ta bukaci kungiyoyin kwadagon da su ci gaba da tattaunawa maimakon shiga yajin aiki, inda ta ce hakan zai yi illa ga tattalin arzikin da ke fama da hauhawar farashin kayayyaki, karancin kudaden kasashen waje da karancin man fetur.
Tinubu ya kare manyan gyare-gyaren da ya yi guda biyu - kawar da tallafin da kuma kula da canjin kudaden waje - yana mai cewa duk da cewa hakan zai haifar da wahalhalu a cikin kankanin lokaci, amma sun zama dole don jawo hannun jari da bunkasa kudaden gwamnati.
Dandalin Mu Tattauna