Da maraicen ranar litinin 2 ga watan Oktoban nan ne kungiyoyin kwadagon su ka sanar da jingine yajin aikin da suka shirya farawa a fadin kasar a yau Talata zuwa nan da wata daya a cikin wata takardar yarjejeniya da shugaban NLC, Joe Ajaero, da babban sakataren kungiyar, Emmanuel Ugboaja sai shugaban TUC, Festus Osifo da Sakatare Janar na TUC, Nuhu Toro suka sanya wa hannu.
Gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyoyin kwadagon dai sun cimma wannan matsayar ce da yammacin ranar Litinin bayan shafe sa’o’i ana tattaunawa don samo mafita, lamarin da ya kai ga dakatar da yajin aikin na tsawon kwanaki 30 a fadin kasar don baiwa gwamnati damar biyan bukatun su da kuma rage radadin da ‘yan kasa ke ciki bayan cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun da shugaba Tinubu ya yi rantsuwar kama aiki.
Kwamared Muhammad Haruna Ibrahim dake zaman shugaban kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i ta Najeriya ya fayyace abunda ake nufi da karin kudin da aka yi wa ma’aikata ga ‘yan Najeriya, yana mai cewa ba ma’aikatan gwamnatin tarayya kawai zasu ci moriyar karin kudin da aka yi ba.
Tuni dai yan Najeriya daga sassan kasar daban-daban suka fara tofa albarkacin bakinsu a game da matakin janye yajin aikin da kungiyoyin kwadagon suka yi inda wasu ke zargin cewa akwai yiyuwar an baiwa kungiyoyin toshiyar baki ne shi ya sa suka janye yajin aikin.
Sai dai, sakataren tsare-tsaren kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Nasir Kabir, ya ce dukkan zarge-zargen cewa sun karbi wani abu daga hannun gwamnati soki burutsu a ke kuma hakan ba zai hana su gabatar da ayyukan su yadda doka ta tsara ba.
Wani abu da ‘yan Najeriya ke ta kwan-gaba kwan-baya a kai shine menene banbanci tsakanin wannan sabuwar yarjejeniyar da aka cimma a yanzu da na baya inda Kwamared Muhammad Haruna Ibrahim dake zaman shugaban kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i ta Najeriya kuma jami’in binciken kudadden kungiyar NLC ya ce kwarai yarjejeniyar yanzu ta banbanta da ta da.
A wani bangare kuwa wasu ‘yan Najeriya musamman ma a arewacin kasar sun ce tsuguni bai kare ba a fafutukar kungiyoyin kwadago, inda Hon. Haruna Dahiru Bindawa ya ce ya yi tsammanin cewa kungiyoyin kwadagon zasu sanya matsalar tsaro a sahun gaba cikin bukatun da suka gabatarwa gwamnati amma sai aka sami akasi.
Sai dai, Kwamred Muhammad Haruna Ibrahim ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta baiwa tsaro mahimmanci duk da cewa babu maganar tsaro a cikin bukatun da suka gabatar mata.
Takardar yarjejeniyar tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadagon mai shafi uku ta kuma samu sa hannun Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong; Karamin Ministan Kwadago, Dr Nkeiruka Onyejeocha; da kuma ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris.
Idan ana iya tunawa, an kafa kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC a matsayin kungiyar kwadago daya tilo a kasar a shekarar 1978. Kafin nan, akwai cibiyoyin kwadago hudu wadanda suka hada da NTUC, Labor Unity Front, United Labour Congress da kuma majalisar ma’aikatan Najeriya wato Nigerian Workers Council.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna