Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Ta Dakatar Da Yajin Aiki Tsawon Kwanaki 30


Zanga-zangar Lumana Ta NLC
Zanga-zangar Lumana Ta NLC

Da yake sanar da sakamakon taron ga manema labarai, Ministan Kwadago da Aiki, Simon Lalong ya ce, “Kungiyoyin NLC da TUC sun amince da dakatar da yajin aikin na tsawon kwanaki 30 da suka shirya yi a fadin kasar. ”

Kungiyar Kwadago, a daren Litinin 2 ga watan Oktoba, ta amince ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a ranar Talata 3 ga Oktoba, 2023.

Hakan ya biyo bayan tattaunawar kimanin sa’o’i biyar da kungiyar kwadagon ta yi da gwamnatin tarayya a dakin taro na shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Abuja.

Da yake sanar da sakamakon taron ga manema labarai, Ministan Kwadago da aiki, Simon Lalong ya ce, “kungiyoyin NLC da TUC sun amince da dakatar da yajin aikin na tsawon kwanaki 30 da suka shirya yi a fadin kasar nan da za a fara ranar Talata 3 ga Oktoba, 2023.”

, Ministan Kwadago da Aiki, Simon Lalong (Facebook/PLSG)
, Ministan Kwadago da Aiki, Simon Lalong (Facebook/PLSG)

Lalong ya ce gwamnati za ta yi dauki dukkan matakan da ya kamata domin ganin an sami nasara mai dorewa.

Sai dai shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ya ce kungiyoyin za su sake duba yarjejeniyar idan har gwamnatin tarayya ta gaza cika bukatunta.

Kafin a cimma yarjejeniyar, kungiyar kwadagon ta yi barazanar ficewa daga taron ne biyo bayan dagewar da gwamnati ta yi na cewa karin albashin na wucin gadi na N35,000 zai yi na tsawon watanni shida ne kacal.

Ma’aikatan sun zargi tawagar gwamnati da yin watsi da abin da aka amince da shi a daren Lahadin da ta gabata cewa za a kara albashin na wucin gadi na N35,000 da ke fadin gwamnati, har zuwa lokacin da za a tattauna tare da aiwatar da sabon mafi karancin albashi daga shekara mai zuwa.

Amma da yake karanta yarjejeniyar fahimtar juna wato MoU, a karshen taron, Ministan Kwadago da Aiyuka, Simon Lalong, ya ce kungiyar kwadagon ta dakatar da yajin aikin na kwanaki 30.

Yarjejeniyar ta kuma umarci Ministan Kwadago da ya duba albashin ma’aikatan jami’o’in da aka hana.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, da Babban Sakatare, Emmanuel Ugboaja ne suka sanya wa hannu; da kuma Shugaban TUC, Festus Osifo, da Sakatare Janar, Nuhu Toro.

Mambobin tawagar gwamnatin tarayya da suka sanya hannu sun hada da ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong; Karamin Ministan Kwadago da Aiki, Dr Nkeiruka Onyejeocha; da kuma ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris.

~Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG