Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Ma’aikatan Kasar Suka Fara


Shugabannin kungiyar ASUU tare da shugaban Majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila yayin wani zaman sulhu da majalisar ta taba shirya wa don kawo karshen yajin aiki
Shugabannin kungiyar ASUU tare da shugaban Majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila yayin wani zaman sulhu da majalisar ta taba shirya wa don kawo karshen yajin aiki

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya ya ce gwamnati da kungiyar kwadago sun cimma matsaya cewa ba za a yi yajin aiki ba har nan da tsawon mako biyu yayin da gwamnati ke kokarin duba korafe-korafensu.

WASHINGTON, D.C. - Gamayyar kungiyoyin ‘yan kasuwa da na ‘yan kwadago sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar sakamakon dakatar da tallafin man fetur.

ABUJA: Ma'aikatan hukumar insuran lafiya sun shiga yajin aiki
ABUJA: Ma'aikatan hukumar insuran lafiya sun shiga yajin aiki

Kungiyoyin sun kuma nemi da a kara musu kudi akan mafi karancin albashin ma'aikatan gwamnati.

A wannan makon, kungiyoyin suka yi kira da a gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.

Zanga Zangar NLC-ASUU 10
Zanga Zangar NLC-ASUU 10

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Samuel Lalong ya shaidawa Muryar Amurka cewa gwamnati ta gana da wakilan kungiyar kwadago a ranar Talata, kuma kungiyar ta amince ta ba gwamnatin kasar mako biyu domin ta magance wasu korafe-korafen na su.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG