Idan ba a manta ba, Ibrahim da Salamotu sun yi aure ne a watan Afrilun 2013, jim kadan bayan aurensa na farko ya mutu sakamakon zargin da ake yi masa na dukar matarsa wanda ya musanta.
A cewar mujallar E24-7, ma’auratan sun fara samun matsala jim kaɗan bayan aurensu saboda bambancin ajin dukiyarsu.
"Salamotu, wacce ta fito daga gidan arziki, ba ta gamsu da yanayin rayuwarta ba a gidan Chatta, kuma hakan ya kawo cikas ga zamantakewarsu har zuwa lokacin da ta fita daga gidan, makwanni biyu da suka gabata." a cewar Mujallar .
Game da zarge-zargen cewa ya auri Salamatu ne saboda dukiyarta, Ibrahim ya ce, “Gaskiya Salamatu kyakkyawar mace ce, kuma ta fito daga gida na masu arziki, amma da na yi niyyar aurenta don kudi, da ma ba zan saurare ta a lokacin da na hadu da ita ba.
Wasu daga cikin masoya na da abokan arziki na iya ba da shaida cewa sama da shekaru biyu na nemi macen da ta dace bayan alakar da ke tsakani na da tsohuwar uwargida ta da zaman aurenmu ya yi tsami. Ni ba mai niman masu arziki ba ne kamar yadda wasu suke rubutawa game da ni.
Ibrahim Chatta mawaki, marubuci, kuma furodusa ne. An haife shi a ranar 13 ga Oktoban 1970 a Bachita da ke karamar hukumar Edu a jihar Kwara, Najeriya. Ya yi fice a fina-finan Yarbawa da yawa.