Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararriyar Mawakiyar Amurka, Selena Gomez Ta Ce Tana Son Fitaccen Mawakin Najeriya, Rema


Selena Gomez Da Rema
Selena Gomez Da Rema

Shahararriyar mawakiyar ta bayyana hake a shafinta na sada zumunta inda ta ce tana kaunar fitaccen mawakin Rema.

WASHINGTON, D.C. - A bayanin nata, Selene Gomez ta godewa Rema da ya zabe ta suka yi waka tare, a wani jerin wakokin da ake dauka a matsayin daya daga cikin manyan jerin wakoki a duniya, ta kuma ce ya canza rayuwarta har abada.

Selena Gomez Tare Da Rema
Selena Gomez Tare Da Rema

Mawakiyar ta kuma dora hotuna guda biyu da suka dauka tare da Rema akan shafin ta, sannan ta rubuta cewa, “Wannan mutumin ya canza rayuwata har abada. Rema, na gode da ka zabe ni muka yi daya daga cikin manyan wakoki a duniya. Ina kaunar ka har abada.

https://www.instagram.com/p/CuLSRvvxGGQ/?utm_source=ig_embed&ig_rid=bc2ea836-7856-4ead-ad96-4d287660271e

Tuni mutane suka fara maida martani, inda a cikin kwana guda da kafa hoton na su da Salena ta yi, sama da mutane miliyan bakwai suka yaba, yayinda da dama suka yaba hadin guiwar tsakanin matasan mawakan.

Rema mai shakaru 23 a duniya ya mayar da martani ga sakon na Gomez, inda ya bayyana tasa kaunar a gare ta a kan shafin na Instagram, yana mai cewa, “ni ma ina kaunar ki Sarauniya ta."

Sakon Instagram tsakanin Selena Gomez da Rema
Sakon Instagram tsakanin Selena Gomez da Rema

An haifi shahararran mawakin wanda ya sami lambobin yabo da yawa, wanda ainihin sunansa Divine Ikubor ne, amma aka fi sanin shi da Rema, ranar 1 ga Mayu 2000.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG