Ba'a bayyana musabbabin mutuwarsa ba, duk da cewarsakon da ta wallafa ya bayyana cewa ya mutu ne a garin Nashville na jihar Tennessee, inda ma'uratan ke zaune.
Harrison ya ba da gudunmowar jini sau 1, 173, a cikin fiye da shekaru 60 bai taba saba alkawarin daukar jinin da aka yi dashi ba har sa'ar da ya yi ritaya a shekarar 2018 yana da shekaru 81.
Shirin fim mai taken “No Other Land,” labarin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da ke fafutukar kare al’ummomin su daga yunkurin rushe su da sojoji Isira’ila ke yi, ya lashe kyautar Oscar ta fitaccen shiri na musamman a ranar Lahadi.
Ayyanawar na kunshe ne a cikin jaridar rundunar ‘yan sandan da aka wallafa a daren jiya Litinin, wacce kakakin rundunar ta jihar Ogun, Omolola Odutola ya yada.
Tems wacce ainihin sunanta shine Temilade Openiyi ta lashe kyautar fitacciyar waka daga nahiyar Afrika mai taken “love me jeje,” inda tayi takara da mawakan Najeriya irinsu Davido da Yemi Alade da Asake da Wizkid da Lojay da kuma Burna Boy.
Marigayi tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter, manomin gaydar da ya lashe zaben shugaban kasar Amurka bayan rikicin Watergate da yakin Vietnam ya mutu a watan Disamban 2024 yana da shekaru 100 a duniya.
Fitacciyar mawakiyar dai ba ta taba lashe kyautar kundin wakoki ba duk da lashe kyautar Grammy 32, fiye da kowane mawaki.
‘Yan sanda a Mumbai sun ce sun kama wani mutum mai shekaru 30 wanda ake zargi da hannu a harin a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP.
Khan mai shekaru 54 na kan murmurewa daga wata jinyar ne, inda itama aka caccaka masa wuka a kashin makarkafarsa, da wuyansa da hannu, kamar yadda likitocin suka shaidawa manema labarai.
Kamar yadda ake faɗa a masna’antar fina-finan Amurka ta Hollywood, dole ne Shirin ya ci gaba. A ranar Litinin, an ba da sanarwar cewa za a ci gaba da shirya bukukwan ba da lambar yabo na Grammys da Oscars kamar yadda aka tsara yi a ranar 2 ga Fabrairu da 2 ga watan Maris.
Za a sanar da sunayen zababbun ne yanzu a ranar 23 ga Janairu, Hukumar Academy of Motion Picture Arts and Sciences ta fada a ranar Litinin Kamar yadda AP ya ruwaito.
Domin Kari
No media source currently available
Ya Fitattun Mutane Ke Amfani Da Kafofin Sadarwa?