Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burna Boy Ya Kafa Tarihin Sayar Da Tikitin Filin Wasan London Mai Cin Mutum Dubu 80 


Burna Boy
Burna Boy

Fitaccen mawakin Najeriya, Damini Ebunoluwa Ogulu, wanda aka fi sani da Burna Boy, ya kafa tarihin zama mawakin Afirka na farko da ya sayar da tikitin filin wasa na London mai daukan mutum 80,000.

WASHINGTON, D. C. - Filin wasan na kungiyar kwallon kafa ta West Ham ne da ke London.

Burna Boy
Burna Boy

Hukumar da ke kula da filin wasan na London ta sanar da hakan a shafinta na Twitter.

A ranar 3 ga watan nan na Yuni Burna ya yi wasansa na kade-kade a filin wasan, wani bangare na rangadin da yake yi, wanda ya yi wa take da “Burna Boy’s Love, Damini Tour.”

Yayin wasan wanda aka yi a ranar Asabar, Burna Boy ya kayatar da masoyansa da fitattun wakokinsa.

Burna Boy
Burna Boy

"SOLD OUT wato an sayar da tikiti na filin wasan kaf!! @burnaboy's RECORD-BREAKING concert, yanzu an sayar da shi gaba da ya a hukumunce!

"Wacce babbar nasara ce ga ɗan wasan Afirka na farko da ya taba tsayawa kwarzo tilo a filin wasa na Burtaniya!" Hukumar filin wasan ta ce.

Wasan ya kuma ya hada da wasu manyan mawaka na duniya irin su Stormzy, Popcaan, da Dave & Jhus wadanda suka taya wannan jarumin na Afirka wajen baiwa dubban masoya kade-kade jin dadi a daren.

Burna Boy
Burna Boy

Magoya bayansa sun rufa mishi baya suna ta rera waka a duk lokacin da Burna Boy ya ke waka, ya yi wakoki sama da 40.

Daga karshe Burna Boy ya ce “Na gode London da Soyayya da kuanar da kuka nuna min da kuma duk wanda ya goyi bayana wajen kafa tarihi!! Sai mun sake haduwa.”

Bayan an kammala wasan wake-waken, an ba Burna Boy lambar yabo da girmamawa.

XS
SM
MD
LG