Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Davido Ya Goge Bidiyon Wakar Da Ya Janyo Ce-Ce Ku-Ce


Davido (Instagram/Davido)
Davido (Instagram/Davido)

Mawakin dai ya cire faifan bidiyon wakar mai suna 'Jaye Lo' mai tsawon dakika 45, wanda ya nuna wasu maza sanye da fararen jellabiya da hula suna tikar rawa a kan shimfidar sallah.

Fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya cire bidiyon da ya wallafa a karshen mako, wanda ya janyo kakkausar suka daga al'umar Musulmi.

Mawakin dai ya cire faifan bidiyon wakar mai suna 'Jaye Lo' da ya wallafa na tsawon dakika 45, wanda ya nuna wasu maza sanye da fararen jellabiya da hula suna tikar rawa a kan shimfidar sallah.

Asalin wakar ta Logos Olori ce, wani sabon matashin mawaki da Davido yake kokarin tallatawa.

Wannan lamari ya sanya Musulmi a fadin Najeriya suna ta sukar mawakan da rashin mutunta addinin Musulunci a cikin wakar.

Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Ali Nuhu, na daya daga cikin wadanda suka fito suka nuna rashin jin dadinsu game da bidiyon wakar.

Ali ya wallafa a shafin na Instagram cewa, “mun gode da goge abun da ka wallafa Davido, ga duk wanda ya ji an bata masa game da abin da ya wallafa a yi hakuri. Mu nuna soyayya, ni ba na jin haushin kowa, amma ina rokonku dukkan masoyana da su daina zagi ko cin mutunci. Na gode.”

Da yake magana game da goge bidiyon, Bashir Ahmad, wanda kwararre ne wajen amfani da kafafan sada zumunta na zamani kuma tsohon mataimaki na musamman ga tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa na zamani, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa “mun yi kokari sosai yadda muka tursasa mawaki Davido dole ya goge videon batanci da ya wallafa a jiya. Allah ya ba mu ikon sanin cewa zaman lafiya da girmama mutuncin juna shi ne kadai hanyar da za ta dawwamar da zaman lafiyar mu a kasar nan.”

Tun bayan da mawakin ya goge bidiyon, yanzu haka kura ta fara lafawa na yadda wasu ke ta suka da yada hoton mawakin da jan fenti a kafafen sada zumunta na zamani.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG