Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sufeton 'Yan sandan Najeriya Ya Ba Da Umurnin Kama Dan Fela


Seun Kuti (Hoto: Instagram/Seun Kuti)
Seun Kuti (Hoto: Instagram/Seun Kuti)

Ana zargin Seun Kuti da cin zarafin wani jami'in dan sanda a Legas, zargin da ya musanta.

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ba Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas umurnin ya kama mawakin Afrobeat, Seun Kuti kan zargin cin zarafin wani dan sanda.

Wani hoton bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a karshen makon nan, ya nuna Kuti yana wanka wa wani dan sanda mari wanda ke sanye da kayan sarki.

Rahotanni sun yi nuni da cewa lamarin ya faru ne akan katafariyar gadar nan ta Third Mainland Bridge da ke Legas a kudancin Najeriya.

“Babban Sufeton ‘yan sandan ya kuma ba da umurnin a kaddamar da cikakken bincike kan abin da ya kai ga cin zarafin dan sandan da kuma hukunta wanda ake zargi.

“Babban Sufeton ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa, ba za su lamunci a rika wulakanta masu rike madafun ikon kasa ba.” Wata sanarwa da kakakin hedkwatar ‘yan sandan Najeriya CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Asabar ta ce.

Rahotanni sun ce Kuti a nasa bangaren ya zargi dan sandan da yunkuri kashe shi da iyalinsa, yana mai cewa a shirye yake ya ba da hadin kai don a gudanar da cikakken bincike.

Seun Kuti, da ne ga fitaccen mawakin Afrobeat, Fela Kuti wanda ya rasu a shekarar 1997.

XS
SM
MD
LG