Jam'iyyar APC a jihar Yobe ta zama ta farko da ta rantsarda shugabanninta a Najeriya tun lokacin da jam'iyyu uku suka hade suka rikide zuwa APC.
WASHINGTON, DC —
An yi taron kaddamar da zababbun shugabannin jam'iyyar APC na jihar Yobe a Damaturu fadar gwamnatin jihar.
Taron ya samu halartar gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Geidam da jigajigan jam'iyyar na kasa da 'yan majalisun jiha da na tarayya da suka fito daga jihar Yobe.
Kwamishanan shari'a na jihar Ahmed Mustapha Gonobe shi ya rantsarda Mai Mala Bunumi a matsayin shugaban jam'iyyar na jihar da wasu talatin da hudu.
A wani abu sabo kuma da ba'a saba gani ba a taron siyasa gwamnan jihar Ibrahim Geidam ya jagoranci addu'a ta musamman dangane da daliban da aka sace a garin Chibok dake jihar Borno. Ya roki Allah ya ba jihar Yobe da kasar zaman lafiya. Ya kuma gargaddi jama'a da su cigaba da addu'a Allah ya dawo da yaran lafiya.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.

Your browser doesn’t support HTML5