Ba za'a gudanar da irin wannan zabe ba, a jihohin Osun da Ekiti, inda ake shirin gudanar da zabubbukan gwamnonin nan da 'yan watanni kadan.
Da yake bayyana wannan ga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-hikaya, daya daga cikin shugabannin jam'iyyar APC na kasa, Kyaftin Bala Jibrin, yace zaben gwamnoni ba wai wani rikicin gida ne ya janyo dage zaben shugabannin jam'iyyar a jihohin Osun da Ekiti ba, sai wannan zabe na gwamnoni da jihohin biyu zasu gudanar saboda sai yanzu ne gwamnoninsu ke cika wa'adin shekaru hudu kan karagar mulki.
Kyaftin Bala Jibrin yace ba su tsammanin samun wata babbar matsala game da wadannan zabubbuka tun da ba na 'yan takarar wata kujerar mulki ba ce, na shugabannin jam'iyya ne. Amma kuma yace tana yiwuwa a samu matsala nan da can saboda watakila wasu da zasu fadi ba zasu ji dadi ba.
Amma dai yace irin abubuwan da aka gani na sauya 'yan takara a can baya kafin hadewar jam'iyyun da suka kafa APC ba zai wakana a wannan karon ba.