Jawabin Goje ya tabbatar da raderadin da aka sha yi cewa akwai baraka tsakanin shugabannin biyu. An ji sanata Haruna Goje yana baiwa mutanen jihar hakuri domin zabo Dankwambo da yayi can baya har ya zama gwamna.
Furucin na Sanata Haruna Goje kuma tsohon gwamnan jihar bai yiwa mukaraban gwamnan jihar na yanzu Hassan Dankwambo dadi ba. Sabili da haka sun kirawo taron manema labarai a Gombe inda suka ce Allah ne kadai ke ba mutum mulki kuma a lokacin da Ya so.
Shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Alhaji Ahmed Yayari yace ya kira taron manema labarai ne ba domin komi ba amma domin kasidar da ya karanta a wata jarida inda tsohon gwamnan Gombe yake nuna bakin ciki akan yadda ya kawo Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo a matsayin gwamnan jihar Gombe. Shi Haruna Goje ya kuma yiwa mutanen Gombe alkawarin fitarda Dankwambo daga mukamin gwamna a zaben shekarar 2015.
Alhaji Yayari yace maganar ta Goje tana kunshe da kuskure da kuma rashin fahimta. Yace tun kafin shekarun Danjuma Goje su kare na zama gwamna al'ummar jihar Gombe suna ta zuwa wurin Dankwambo a Abuja suna matsa masa ya fito ya nemi mukamin gwamnan jihar. Yace a lokacin kowa ya san Haruna Goje ya so sirikinsa ya gajeshi a matsayin gwamna amma Allah bai yadda hakan ya faru ba. Abun da yake so Allah bai yadda da shi ba.
Akwai rashin gamsuwa daga wasu al'ummar jihar Gombe lokacin da Danjuma Goje ya zama gwamna a shekarar 2003. An yi sharia har zuwa kotun koli kuma sai shekarar 2007 aka tabbatar masa da kujerar. Amma da aka zabi Dankwambo a shekarar 2011 babu wani dan takara da ya kaishi kara yace bai yadda da zabensa ba kamar yadda aka yi lokacin Goje.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.