A jihar Gombe misali, jagoran jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Senata Muhammad Danjuma Goje shine ya yaye kallabin shirin gudanar da zaben.
Wani jigo a jam’iyyar, kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar tarayya, Usman Bayero Nafada, yayi tsokaci akan karbuwar jam’iyyar a jihar Gombe.
“Abinda muka gani, zaku iya bada labarin cewa canji, kamar yazone a jihar Gombe, illa dai ana jiran lokaci,” inji Mr. Nafada.
Majidadin Gombe, Injiniya Sa’adu Abubakar Abdullahi, jigo ne a jam’iyyar amma ya kauracewa zaben. Ko meyasa?
“Dalilinmu dai shine, shinfidin zaben wato shugabancin kasa ba’a yi shi ba tukunna, kaga idan mun shiga, kamar mun yi amai ne mun kwashe,” Mr. Sa’adu Abubakar kennan yake mayar da martani.
To sai dai kuma a jihar Bauci, an samu rudani wajen gudanar da zaben, saboda karar da wasu ‘yan jam’iyyar suka shigar kotu domin ta tsayar da zaben. Daga bisani dai an gudanar da zaben cikin dare, zuwa wayewar Lahadinnan. Yanzu haka ana jiran sakamakon zaben.