A wani gangami na nuna goyon baya wa gwamnan Borno jam'iyyar APC ta buga kirjin samun nasara cikin duk zabubukan da za'a gudanar a shekarar 2015
WASHINGTON, DC —
Jam'iyyar APC a jihar Borno ta ce tana da kwarin gwiwa zata lashe zabubukan gama gari da za'a yi a shekarar 2015.
Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Borno Alhaji Abu Kyari ya bayyana hakan bayan ya jagoranci wani gangami na nuna goyon baya wa gwamnan jihar Kashim Shettima. Ya ce taron ya nuna irin goyon bayan da gwamnan ke da shi sabili da irin ayyukan da ya yiwa mutane. Mutane sun yadda da shi kuma sun amince. Sabili da haka suna godiya ga Allah da irin goyon bayan da mutane suka baiwa gwamnan. A kasar Borno gwamnan shi ne jagoran jam'iyyar APC.
Wani Onarebul Ciroma Usman ya ce jam'iyyar APC taimako ce daga Allah domin ya ceci mutanen jihar daga hannun mutanen dake zaluntar kasar. Dangane da rigingimu dake cikin jam'iyyar ya ce ko mata da miji ma suna samun rigima kafin su warware. Matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta ba matsaloli ba ne da zasu cigaba ba.
Wani Rabiu Useini cewa ya yi gwamnati ta shiga cikin rikici ta samu gari cikin yamutsi amma duk da haka gwamnan jihar na iyakacn bakin kokarinsa. Tun da ya shigo mulki inda ba wasu watanni biyar da suka wuce ba babu lokacin da ba'a samu tashin hankali ba.
Ga rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5