Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Atiku Abubakar Sun Mayarda Martani Kan Canza Sheka


Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Yayin da jam'iyyar APC ke ganin cewa samun Atiku Abubakar ya fi asarar ficewar Bafarawa da Shekarau daga jam'iyyar, magoya bayan Atiku Abubakar kuma suna cigaba da mayarda martani kan canza shekar da ya yi.

Magoya bayan tsohon mataimakin kasar Najeriya Atiku Abubakar sun fara mayarda martani kan canza shekar da ya yi daga PDP zuwa APC.

Aminu Gwandu shugaban magoya bayan Atiku Abubakar ya ce halin da Najeriya ke ciki yanzu shi ya sa suka ga ya kamata a hadu tare a tsira tare. Dangane da cewa ko Atiku Abubakar ya shiga APC ne domin ya dinga harzuka rikici ya kare irin su Janaral Buhari kamar yadda ya yi cikin PDP sai Aminu ya ce sun san cewa akwai kyakyawar fahimta tsakaninsu. Ya ce sun tabbatar cewa Janaral Buhari da Atiku Abubakar suna cikin APC ne tare sabo da kasa da cigaban 'yan Najeriya.

Barrister Tanko Isa ya fara ne da habaici ya ce akuya bai kamata ta zauna cikin kuraye ba. Ya ce dole su jawo Atiku Abubakar daga cikin kuraye su sashi cikin akuyoyi. Da aka fada masa cewa APC na son Atiku Abubakar ne domin yana da kayan aiki ba wai siyasar gaskiya ya keyi ba sai ya ce siyasar gaskiya ya keyi kuma ai PDP mai mulki ita ce ke da kayan aiki. Amma a daina bintu domin babu adalci.

Amma wani matashin 'dan siyasa daga yankin arewa maso gabas inda Atikun ya fito Yusuf Lamido Kitere na ganin akwai bukatar yin taka tsantsan da yawan canza sheka. Ya ce su matasa dake tasowa ganin yadda halin da kasar ke ciki basu ga alamar zasu iya yin guje-guje ba ko bin masu guje-guje daga wannan siyasa zuwa waccan. Ya ce yanzu jihar Adamawa ta koma baya amma fatansu shi ne mayan zasu gyara gida. Kodayake ya yi wasu abubuwa masu kyau a jihar basa son ya bar PDP domin inda ya je yanzu bashi da gurbi domin APC jam'iyya ce ta mutanen da ke da buri mai tsananin gaske. Ya ce idan an shigo cikinsu idan ba sa'a mutum ya yi ba to karshenta sai sun rusa mutum. Kuma ba'a yiwa dan siyasa fatan hakan ya faru. Ana yi masa fatan karko mai kyau amma fa sai ya samu zaunuwa a inda yake da mutunci.

Sai dai 'yan siyasa na ganin APC ta fanshe asarar ficewar Bafarawa da Shekarau da samun Atiku Abubakar.Amma duk da haka wani jigon APC Dr. Ibrahim Yakubu Lami ya caccaki wadanda suka bar yam'iyyar. Ya ce abun da suka yi abu ne na ban tausayi kuma zasu yi hawaye.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG