Sanato Ndumi ya ce abun damuwa ne matuka kan irin halin da mutanen yankin ke ciki. Ya ce duk da suna cikin mugun talauci amma babu wani abu takamaimai da gwamnati tarayya ta yiwa shiyar ganin cewa a bayyane take cewa shiyar ce tafi kowace talauci kuma yankin ne ke cigaba da fama da tashe tashen hankula da hare-haren 'yan bindiga. Ya ce an yi kone kone da kashe kashe. Manya manyan kasashen duniya sun ce ya kamata a bada taimako na musamman ga shiyar domin a habbaka arzikin yankin a kuma tallafawa mutane.
Yankin arewa maso gabas na cikin kidigdigar da hukumar majalisar dinkin duniya ta yi inda ta nuna cewa yankin na cikin wadanda talauci ya fi yi masu katutu a duniya. Sabili da haka ma Ndume ya ce yakamata gwamnatin tarayya ta dauki wani mataki musamman. Amma gwamnati na nuna masu wariya kamar yankin baya cikin Najeriya. Ya ce duk 'yan Najeriya suna karkashin shugaban kasa. Hakin kowa na kan shugaban kasa. Kowane bangaren Najeriya nada haki a kasar. Ya ce ba wai an mayarda su saniyar ware ba ma gwamnatin ta yi watsi da su. Ya ce a akasarin gaskiya ba'a yi masu adalci ba.
Taimakon nera biliyan biyu da gwamnatin tarayya ta baiwa shiyar tamkar digo ne domin bai taka kara ya karya ba a ganin Sanato Ndumi.
Ga cikakken rahoto.