Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senatoci 11 a Majalisar Dattawan Najeriya Sun Koma APC


APC
APC

Akwai alamun cewa ba’a kawo karshen rikicin siyasar da jam’iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta kwashi lokaci mai tsawo tana fama da shi ba, domin kuwa a sanyin safiyar yau ne, jam’iyyar ta rasa ‘yayanta goma sha daya a majalisar dattawa.

Wannan ya bayyana ne a wata wasikar canza sheka, mai dauke da sa hannun ‘ya’yan majalisar dattawan su goma sha daya da suka aikawa shugabansu David Mark, cewa daga yau sun koma jam’iyyar adawa ta APC.

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Danjuma Goje yana daga cikin wadanda suka canza sheka daga PDP zuwa APC. Yace “muna da yawa, mun fi sha daya amma sha daya ne suka sa hannu, saura suna zuwa daga baya. A cikin kwanakinnan, akwai masu zuwa, hudu ko biyar ko shida, koma fiye da haka. Suna zuwa, amma mune dibar fari”.

Mr. Goje ya kara da cewa “abun mamaki shine har yanzu, mun dauka cewa shi shugaban majalisa zai karanta sunayenmu mu goma sha dayannan, amma bai karanta ba. Ta yiwu Gobe, zai karanta.”

“Tsohon gwamnan jihar Kwara Saraki yana ciki, da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Senata Abdullahi Adamu, yana ciki. Akwai Jibrilla daga Adamawa, akwai Senata Muhammad Ali Ndume daga Borno, da Senata Aisha Jummai Alhassan daga Taraba, akwai Senata Ummaru Dahiru daga Sokoto, akwai Senata Ibrahim Gobir daga Sokoto, akwai Senata Lafiyaji daga Kwara, da Senata Wilson daga Rivers, da kuma Senata Magnus Abe daga Rivers.”

Kafin wannan guguwar canji ta shafi majalisar dattawan, jam’iyyar PDP na da wakilai 73, APC kuma na da 33. Da wannan canji a iya cewa, jam’iyyar Adawa ta APC yanzu ta samu wakilai 44 kennan, a majalisar dattawan. Duk da haka, APC bata samu rinjaye ba.

Wannan lamari dai ya saka jam’iyyar PDP, baza ta iya samun kuri’a biyu bisa uku a majalisar dattawan ba, a lokacin da za’a bukaci haka, domin shigar da kudurorin shugaba Goodluck Jonathan guda biyu dake gabansu, wato na tantance ministoci, da kuma na kasafin kudin bana.
XS
SM
MD
LG