Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Shugaban Kasa Nada Hurumin Shirya Taron Kasa?


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Har yanzu masana harkokin sharia na muhawara kan ko shugaban kasa nada hurumin shirya taron kasa a karkashin kundun tsarin mulkin Najeriya

Har yanzu ba'a daina gutsuri tsomi a kan hurumin da shugaba Jonathan ke da shi na shirya taron kasa ganin cewa ana da zababbun wakilan jama'a a majalisun tarayya da na jihohi.

Yushau Waziri Mamman lauya mai zaman kansa kuma kwararre a fashin bakin kundin tsarin mulkin kasa ya yi karin haske. Ya ce kundun tsarin mulkin Najeriya ya bashi dama ya kafa irin wannan taron. Tsarin mulkin ya ce shugaban kasa na iya yin duk abun da zai kawo zaman lafiya da cigaba da tsaro a kasa. Ya ce bayanin da sakataren gwamnati ya yi ya ce za'a yi taron ne domin cigaban kasa kuma ba za'a taba batun raba kasa ba. Taron zai tattauna ne kan abubuwan da zasu kawo zaman lafiya da cigaba. Sabo da haka abun da shugaban kasa ya shirya yi yana da kyau sai dai ba'a san abun dake cikin zuciyarsa ba.

Dangane da anfanin majalisun kasa Barrister Mamman ya ce su dokoki su keyi. Basu tattauna abubuwan da taron zai maida hankali a kai. Sabo da haka idan an tattauna yadda ya kamata 'yan majalisun zasu dauki abubuwan da aka tattauna su mayarda su doka. Abubuwan da 'yan Najeriya suka amince da shi a cikin tattaunawar sai su yi doka kasa ta yi anfani da shi.

Amma wasu jihohi da wasu jam'iyyu sun ce babu ruwansu da taron duk da rungumar da wasu masu son taron suka yiwa taron. Dr. Abubakar Kari kwararre a kan zamantakewar jama'a kuma malami a Jami'ar Abuja ya ce babu wata magana ko matsala da suka fi karfin manya mayan hukumomi na siyasa da kuma na gwamnati musamman majalisun jihohi da na tarayya. Babban aikinsu ne su rika zakulo batutuwa suna tattaunawa ana samun matsaya agame dasu. Saboda haka idan wani ya ce za'a yi wani taro wanda akwai shakku bisa halarcinsa da shakku bisa jagorancinsa da shakku bisa wakilcinsa kuma shi taron ne zai tattauna abubuwan da yakamata majalisu su tattauna to lallai akwai wani abu daban.

Kan batun wakilci Dr Kari ya ce bayanin da aka fitar makon jiya ya sa alamun tambayyoyi da dama kuma masu daure kai. Daya daga ciki shi ne wakilcin taron. Cikin wakilai 492 mafi yawa jami'an gwamnati ne zasu nada su, wato shugaban kasa da gwamnoni da shugabanni na wasu sashen gwamnati ko kuma wadanda ke kusa da gwamnati. Wannan shi ne ke bada tabbacin akwai wani abu a kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG