APC: Ana Cece-ku-ce Kan Kudaden Sayen Fom Din Takara

Jiya jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fitar da jadawalin zaben fitar da ‘yan takara a matakai daban daban tare da bayyana kudaden da kowane dan takara zai kashe ya sayi fom din shiga zabe.

Masu sharhi a fagen siyasa a Najeriya sun fara tsokaci dangane da kudaden sayen fom na neman takara da jam'iyya mai mulki ta APC ta fitar a Najeriya.

"Wannan tsawwala kudi na APC, daurewa siyasar kudi da ta ubangida gindi ne, wanda ba shi da kudi dole zai nemi ubangidan da zai saya masa." Inji Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, malami da ke koyar da kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero a wata hira da suka yi da Mahmud Ibrahim Kwari.

Ya kara da cewa, "sannan hakan, rufe kofa ne ga mutane da yawa su shiga siyasa a dama da su."

Shi kuwa, Dr. Sani Lawan Malumfashi, wanda tsohon shugaban hukumar zabe ta jihar Kano ne, ya kalli lamarin ta fuska biyu.

"Ta fannin bai wa 'ya'yan talakawa dama da matasa, ba ya kan turba, kuma a cikin matasan nan akwai masu kafin basira." Dr. Malumfashi ya bayyana a hirarsa da Mahmud Ibrahim Kwari.

Sai dai a ganin Dr Malumfashi, "amma ta fannin tsarin dimokradiyya kuma, yana kan turba, saboda tsari ne mai tsada kamar yadda kowa ya sani

Masana kimiyyar siyasa da masu sharhi a fagen demokaradiyyar kasar sun fara tsokaci game da batun.

A cikin wata sanarwa ne da sakataren tsare-tsare na Jam’iyyar ta APC ya sanyawa hannu ta ce mai neman takarar shugaban kasa zai sayi fom din shiga neman takara akan Naira miliyan 45.

Sannan mai neman gwamnan jiha Naira miliyan 22.5 kana kujerar Sanata Naira miliyan 7, yayin da dan majalisar wakilai zai biya Naira miliyan 3.8

Yayin da wanda ke neman kujerar majalisar dokoki ta jiha a karkashin inuwar Jam’iyyar ta APC zai sayi fom na shiga zabe akan kudi Naira dubu 850.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

APC: APC: Ana Cece-ku-ce Kan Kudaden Sayen Fom Din Takara