Al’ummomi sun shirya wani gangami a jihar Taraba, a arewa maso gabashin Najeriya. Baya ga Kamaru, a Najeriya kusan kananan hukumomi 16 ne na jihohi biyar ke cikin wannan batu.
Yankunan sun hada da yankin kananan hukumomin Mubi ta arewa da Mubi ta Kudu, Michika, sai karamar hukumar Toungo, da Ganye da kuma kananan hukumomin Gashaka, Kurmi, Sardauna a jihar Taraba da ma wasu jihohin Najeriya. Waddanan yankunan na fatan suma su sami 'yancin kansu.
Su dai al’ummomin ,sun soma tarukan bita da kuma fadakar da juna a Najeriya, biyo bayan taron da suka gudanar a Bamenda na kasar Kamaru domin tunawa kasashen biyu yarjejeniyoyin da aka kulla da Majalisar Dinkin Duniya a shekarun baya.
Kamar yadda aka saba, a irin wannan gangami shugaban wannan fafutukar wanda har ila yau ke yiwa Majalisar Dinkin Duniya aiki a matsayin jami’in tuntuba ta fannin diflomasiya, Farfesa Martin Chia Ateh, ya kan turo da sako na musamman, inda a wannan karon ya ce zasu ci gaba da fadakarwa.‘’Dole a ci gaba da fadakar da al’umma,tunda ba tun yau ba kotun duniya ta bada hukunci kan lamarin kuma duk kasashen da abun ya shafa sun sani har ma yana cikin taswirar duniya", injishi.
‘’ Ya kamata wadannan kasashen biyu, wato Kamaru da Najeriya su bada hadin kai don mu samu 'yancin kanmu,kamar yadda suka rattaba hannu a yarjejeniyar da aka yi da Majalisar Dinkin Duniya, biyo bayan hukuncin kotun duniya", a cewar Farfesa Martin Chia Ateh, wanda shine shugaban wannan fafutuka.
Facebook Forum