Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaftare Tallafin Hukumar Agaji Ta MDD Da Amurka Ta Yi, Ya Haifar Da Cikas


Hukumar agaji da ayyuka a yankin Palasdinawa ta MDD tace ta samu rage gibin kasafin kudi na dala miliyan dari hudu da arba’in da shida da aka samu sakamakon zaftare tallafin Amurka da gwamnatin kasar tayi, sai dai bata sami nasarar cike gibi bakin daya ba.

Tace karancin kudin da aka samu zai iya shafar ayyukan da hukumar ke gudanarwa a sansanan ‘yan gudun hijira na Palasdinawa a duk fadin gabas ta tsakiya.

Hukumar ta sanar da cewa, ta tara dala miliyan dari biyu da talatin da takwas daga kasashen Qatar da Saudiya da Japan da KTT, da kuma Canada. Bisa ga cewar hukumar, yanzu ana da gibin dala miliyan dari biyu zuwa karshen shekara.

Da yake Magana jiya talata babban kwamishinan hukumar Pierre Krahenbuhli ya bayyan takaicin shawarar da Amurka ta tsaida na daina tallafawa ayyukan da hukumar ke gudanarwa a madadin ‘yan gudun hijira Palasdinawa kimanin miliyan biyar. Ya kuma bayyana cewa, tilas ne a nemi wata hanyar samun kudi domin a taimakesu.

Yace batu ne na mutunta ‘yan gudun hijirar, da kuma batun tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin. Kun sani muna aiki ne a daya daga cikin wurare da aka fi fama da banbancin ra’ayi a duniya.

Amurka ta zaftare tallafin da take ba hukumar agaji da gudanar da ayyuka a yankin Palasdinawa ranar 31 ga watan Agusta. Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert tace Amurka ba zata ci gaba da samar da kudi a shirin dake cike da kurakurai ba.

Masu kula da lamura sunce Amurka ta zaftare kudin ne da nufin matsawa Palasdinawa lamba su koma teburin tattaunawa da Isra’ila.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG