Ana Zargin Kusan Mutane 30, 000 Sun Kamu Da Cutar Kyandar Biri A Nahiyar Afrika A Bana - WHO

Democratic Republic of Congo, August 24, 2024.

WHO ta kara da cewar, a wannan 'dan tsakani fiye da mutane 800 ne suka mutu sakamakon cutar da ake zargin kyandar biri ce a nahiyar Afirkan. Haka itama makwabciyar Congon, jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fama da karuwar barkewar cutar.

Cutar kyandar biri na iya yaduwa sanadiyar mu’amala da kut da kut. Bata da tsanani amma a wasu lokutan tana kisa. Tana haddasa yanayi irin na mura da kuraje irin na kwazowa a sassan jiki.

Sanarwar ta WHO ba ta bada alkaluman yadda yaduwar cutar ta kasance a shekarun baya ba. Sai dai hukumar lafiya ta tarayyar Afirka tace a bara an samu mutane 14, 957 da suka kamu da cutar sannan an samu rahoton mutuwar mutane 739-an samu karuwar kaso 78.5 cikin 100 na samun sabbin wadanda suka harbu da cutar daga shekarar 2022.

Congo Mpox

A cewar rahoton na WHO, an samu mutane 29, 342 da ake zargin sun kamu da cutar sannan ta hallaka 812 daga watan Janairu zuwa Satumbar bana.

A cewar WHO, an samu rahoton dake tabbatar da cewar jumlar mutane 2, 082 sun kamu da cutar a fadin duniya a watan Agusta kawai, adadi mafi yawa tun bayan watan Nuwambar 2022.

A Asabar din da ta gabata, asusun yaki da annoba na bankin duniya yace zai bayar da dala milyan 128,89 ga kasashen Afrika 10 domin tallafa musu a yaki da cutar.

-Reuters