Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO Ta Kira Taron Gaggawa Kan Yaduwar Cutar Kyandar Biri A Nahiyar Afirka


Sabon nau'in cutar mpox a Congo
Sabon nau'in cutar mpox a Congo

Cibiyar Kula da ke yaki da cututtuka da kariya ta Afirka ta bayyana a wannan makon cewa karuwar yaduwar kyandar biri a fadin nahiyar wani lamari ne da ke bukatar matakan gaggawa.

Cibiyar ta kara da cewa kwayar cutar na iya yaduwa a kan iyakokin kasa da kasa.

A ranar Laraba, Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kiran a hada taron kwararru don yin la'akkari da yin irin wannan sanarwar gaggawa kan cutar.

Africa Mpox
Africa Mpox

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce an samu fiye da mutum 14,000 da suka kamu da cutar, da kuma mutuwar mutum 524 wadanda tuni suka zarce adadin na bara.

Ya zuwa yanzu dai, fiye da kashi 96% na duk lokuta da mace-mace suna cikin ƙasa guda wato Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo.

Masana kimiyya sun damu da yaduwar sabon nau'in cutar a kasar, wanda zai iya yaduwa cikin sauƙi tsakanin mutane.

Yara sun fi saurin kamuwa da sabon nau'in mpox a Congo
Yara sun fi saurin kamuwa da sabon nau'in mpox a Congo

Ko me muka sani game da kyandar biri?

Masana kimiyya sun fara gano cutar ne a shekara ta 1958 lokacin da aka sami bullar wata cuta mai kama da “kyanda” a cikin birrai.

Har zuwa kwanan nan, ana ganin galibin mutanen da suka kamu da cutar a cikin mutane a tsakiyar Afirka da yammacin Afirka ne waɗanda ke da kusanci da dabbobi masu kamuwa da cuta.

Masana, masu bincike akan MPOX
Masana, masu bincike akan MPOX

A cikin shekarar 2022, a karon farko, an samu tabbacin za a iya yada cutar ta hanyar jima’i lamarin da ya haifar da barekwar cutar a sama da kasashen 70 wadanda a baya ba su da cutar.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG