Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yiwuwar Barkewar Annobar Kyandar Biri A Najeriya – Hukumomin Lafiya


FILE PHOTO: The hands of a patient with skin rashes caused by the mpox virus are pictured in Kinshasa
FILE PHOTO: The hands of a patient with skin rashes caused by the mpox virus are pictured in Kinshasa

Gwajin cutar kyandar biri (mpox) da kuma sanya ido sosai don gano wadanda ke dauke da cutar a bakin iyakokin Najeriya na daga cikin matakan gaggawa da hukumomin Najeriya da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika ta CDC ke dauka don dakile yaduwar sabon nau'in cutar.

A dakin gwaje-gwajen cututtuka na kasa na Najeriya da ke birnin tarayya Abuja, ma'aikatan lafiya suna yin gwajin cutar kyandar biri da ake kira mpox cikin sauri.

Matakin dai na zuwa ne bayan da hukumar sa ido kan cututtuka masu yaduwa ta Afirka ta CDC a makon da ya gabata ta ayyana cutar a matsayin mai barazana ga lafiya sosai.

Cutar kyandar biri cuta ce mai saurin yaduwa da ke haddasa kuraje masu fidda ruwa a jikin bil’adama.

Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu babu wanda ya kamu da sabon nau’in cutar a kasar.

Yayin da ake gwajin cutar don samun sakamako cikin sauri a kasar, hukumomi na sa ido sosai kan jihohi 9, ciki har da Legas da babban birnin tarayya Abuja.

Hukumomi suna kuma rarraba kayan gwajin cutar ga jihohin da ke tattare da hadarin cutar sosai, don taimaka wa wajen gano cutar cikin sauri da samar da magani, da fadakar da jama'a.

Likita Robert Musole a kauyen Kavumu da ke jamhuriyar dimokradiyyar Congo.
Likita Robert Musole a kauyen Kavumu da ke jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

Jide Idris, babban Daraktan Hukumar CDC ta Najeriya, ya ce ya zuwa yanzu a wannan shekarar, hukumar ta samu rahoton mutane 39 kacal da suka kamu da cutar mpox, kuma ba a samu mace-macen da ke da alaka da cutar ba, amma ya yi gargadin cewa yana da muhimmanci a sa ido sosai.
"Saboda mutanen da ke zuwa daga waje, matafiyan da musamman ke zuwa daga wuraren da aka sami barkewar cutar sosai, akwai bukatar mu tabbatar da cewa mun bi diddigi don dakile yaduwar cutar a cikin kasar, musamman nau’in cutar na Clade 1," a cewar Idris.

Babbar hukumar ta kula da lafiyar jama'a ta Afirka ta ayyana cutar mpox a matsayin mai barazana ga lafiyar al’umma, bayan da ta tabbatar da cewa mutane kusan 3,000 sun kamu da cutar sannan wasu sama da 500 sun mutu a kasashe 13 na Afirka a wannan shekarar ta 2024.

Kwayar cutar kyandar biri
Kwayar cutar kyandar biri

Cibiyar CDC ta Afirka ta yi gargadin cewa sabon nau'in cutar, wanda aka fara gani a jamhuriyar dimokradiyyar Congo, shi aka fi saurin kamawa a baya-bayan nan kuma yara sun fi fuskantar hadarin kamuwa da shi.

Kwararre a fannin cututtuka a cibiyar kula da cutar SIDA ta Afirka ta Kudu, Salim Abdool Karim, ya yi gargadin cewa akwai bukatar a tashi tsaye wajen yin gwajin cutar.

"Hujjojin da muka tattara akan adadin wadanda suka kamu da cutar, da mace-macen da aka samu kadan ne daga cikin abubuwan da ke tattare da babban kalubalen. Kuma dalilin shi ne alamomin cutar mpox ba su da tsanani sosai, ba a sa ido sosai, bamu da isassun kayan aikin gwajin cutar da ake bukata, da bin diddigin wadanda suka yi mu’amulla da wadanda suka kamu da cutar da kuma sanar da hukumomi,” a cewar Salim.

Mara lafiya mai fama da mpox a asibitin Kavumu, jamhuriyar dimokradiyyar Congo.
Mara lafiya mai fama da mpox a asibitin Kavumu, jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

Sai dai manazarta sun ce nuna kyama ko wariya da bayanan karya na iya kawo cikas ga kokarin da kasar ke yi na dakile yaduwar cutar mpox.

"Akwai bukatar a samar da wasu hanyoyin tura sakon gargadi don ya kai ga matakin karkara, ta yadda za a iya dakile cutar, amma amfani da gidajen rediyo da talabijin ba za su isa ba," a cewar Chris Sunday, wani mazaunin birnin Abuja.

A shekarar 2020, hukumar lafiya ta duniya ta WHO ta ayyana mpox a matsayin cutar da ke barazana ga lafiyar al’uma bayan aka sami rahoton bullar cutar a kasashe sama da 70.

Yayin da Najeriya ke shirin fuskantar yiwuwar barkewar cutar, masu sharhi kan harkokin lafiya sun ce akwai bukatar a kara daukar matakan kariya, kuma akwai bukatar kamfanonin kasa da kasa su kawar da barazanar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG