Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Za Ta Ba Afirka Tallafin Allurar Rigakafin Cutar Kyandar Biri


JYNNEOS Allurar Rigakafin MPOX
JYNNEOS Allurar Rigakafin MPOX

Jamus za ta ba da gudummawar alluran rigakafi 100,000 na cutar kyandar biri wato mpox daga hannun jarin sojojinta don taimakawa wajen shawo kan barkewar cutar a nahiyar Afirka na cikin kankanin lokaci tare da ba da taimako ga kasashen da abin ya shafa, in ji kakakin gwamnati a ranar Litinin.

Gwamnati za ta bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya da wasu sassauƙan hanyoyin kuɗi ta hanyar kayan aiki daban-daban don yaƙar cutar ta mpox da kuma tallafawa abokan haɗin gwiwarta a Afirka ta hanyar haɗin gwiwar rigakafin GAVI, in ji kakakin.

Annobar cutar kyandar biri a Congo
Annobar cutar kyandar biri a Congo

Jamus tana da kusan allurai 117,000 na Jynneos, wanda sojojin Jamus ke tarawa tun bayan da Berlin ta sayo su a cikin shekarar 2022.

Kasar ta ce adana wani kaso na allurar, don kare hukumomi masu balaguro, in ji mai magana da yawun ma'aikatar tsaro a ranar Litinin. Ya kara da cewa dole ne a yanke shawara ta daban idan ana batun sake yin odar alluran rigakafi.

Congo Mpox
Congo Mpox

Hukumar lafiya ta duniya dai ta ayyana mpox a matsayin annobar gaggawa akan kiwon lafiyar jama'a a duniya bayan barkewar cutar a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo zuwa kasashe makwabta da wani sabon nau'in kwayar cutar ya bullo, “Clade Ib”, wanda ya haifar da damuwa kan yadda yake saurin yaduwar cutar.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG