Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya bayyana yakinin cewa za’a iya kawar da annobar kyandar biri a nahiyar Afirka nan da watanni shida masu zuwa.
Babban Daraktan hukumar ta WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya fada a ranar Juma'a cewa, ana sa ran kashin farko na alluran rigakafin hukumar zai isa kasar Congo nan da ‘yan kwanaki.
Afirka ta sami wani sashe kalilan kawai na alluran rigakafin da ta ke bukata, domin rage yaduwar cutar.
Kasar Congo ce ta fi yawan kamuwa da cutar - tare da mutane 18,000 da ake zargin sun kamu, yayin da mutane 629 suka mutu.
WHO ta ayyana barkewar cutar kyandar biri a Afirka a zaman matsayin shirin gaggawa na duniya, tare da fatan hakan zai haifar da martani mai karfi a duniya game da cutar a nahiyar, inda ta ke yaduwa ba tare da an sani ba tsawon shekaru.
Dandalin Mu Tattauna