Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan IPOB din sun fito da mutanen ne daga cikin wani babban gida, suka yi musu tsirara, suka daddaure su kana suka yi musu yankan rago, a kauyen Igbariam da ke cikin karamar hukumar Oyi ta jihar Anambra.
Wadanda aka kashe din duk iyalan gida daya ne, da suka hada da mata 12, maza 7 da kuma yara kanana da ba’a bayyana adadinsu ba.
Jaridar DAILY NIGERIAN da ta nuna hotuna masu munin kallo na mutanen da aka yanka, akasarinsu mata da yara kanana, ta ruwaito wani daga cikin iyalin gidan yana cewa “sun cire kawunan maza 3, suka kuma ciccire al’aura da sassan jikin wasu mata suka tafi da su.”
Karin bayani akan: IPOB, jihar Anambra, Biafra, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Majiyar ta ce ‘yan ta’addar sun kuma kashe shanu 25, suka raunata 19, kana suka yanka wasu 5.
Yanzu haka kuma wasu yara biyu suna kwance a asibiti sakamakon raunin da suka samu a wannan farmakin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar aukuwar lamarin ta bakin kakakin ta Ikenga Tochukwu, duk da yake a nata bangare, cewa ta yi mutane 9 aka kashe.
Tochukwu ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Monday Bala-Kuryas, ya ba da umarnin kafa runduna ta musamman cikin gaggawa, domin bincike da hukunta wadanda suka aikata danyen aikin.
A cewar sanarwar ta ‘yan sanda, wata tawagar jami’ai a karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda tuni ta ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda suka soma binciken farko nan take.
Ya kara da cewa tuni kuma da aka yi kokarin daidaita al’amura a yankin, haka kuma an kara tsaurara matakan tsaro domin kare aukuwar irin wannan lamarin.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne dauke da muggan makamai na gargajiya da na zamani, inda suka rufarwa babban gidan da kusan dukkan mazaunansa Fulani ne.
Kungiyar ta IPOB da gwamnatin Najeriya ta ayyana a zaman kungiyar ta’addanci, tana ci gaba da kai hare-hare kan ofisoshin jami’an tsaro, hukumomi da kuma daidaikun jama’a.
Na baya-bayan nan shi ne farmakin da suka kai tare da kona gidan gwamnan jihar Imo, bisa zargin yana da hannu a kisan da jami’an tsaro suka yi wa kwamandan kungiyar Ikonson a karshen mako.
Ku Duba Wannan Ma Kungiyar Fafutukar Kafa Biafra Ta Yi Sabon Kwamanda