Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kafa Tuta A Wasu Yankunan Jihar Neja


Gwamnatin jihar Nejan Nigeria ta bada tabbacin cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun shiga jihar sun kwace wasu garuruwa da dama daga hannun mahukuntan jihar.

Dama dai tun a baya ne aka yi ta yayata jita-jitar cewa mayakan kungiyar ta Boko haram sun kafa sansani a jihar Nejan mai iyaka da Abuja fadar gwamnatin Najeriya.

A yanzu dai gwamnan jihar Nejan Alh. Abubakar Sani Bello ne da kansa ya tabbatar da cewa, mayakan kungiyar ta Boko haram sun kafa tutocinsu a wasu garuruwa na yankin karamar Hukumar Shiroro da Muya.

Sh ma shugaban wata kungiyar matasa a yankin na shiroro, Jibrin Abdullahi Tafidan Alawa, yace a yanzu haka yan kungiyar ta Boko haram sun kame mazabu guda 7 daga cikin 8 dake cikin karamar Hukumar Shiroron..

Jihar Nejan dai ta zama wani sansani na 'yan ina da kisa inji wani mazaunin garin Gulbin Boka a yankin karamar hukumar Mariga da ya nemi a sakaya sunansa yace ko a daren ranar lahadin nan maharan sun kashe masu mutane 11 tare da kore masu shanu masu tarin yawa.

A yanzu dai da dama daga cikin manyan garuruwa a jihar Nejan makare suke da 'yan gudun hijira da suka tsere daga kauyukkansu saboda hare haren yan bindigar.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG