A jiya ne rundunar sojin Najeriya ta ba da sanarwar cewa ta jagoranci wata tawagar jami’an tsaro, a wani samame kan shelkwatar mayakan kungiyar ta IPOB a kauyen Awomawa da ke karamar hukumar Oru ta Gabas ta jihar Imo.
Rundunar sojin ta ce ayarin jami’an tsaron da suka kumshi sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an tsaro na farin kaya – DSS, sun sami nasarar kashe Ikonson Commander da wasu manyan kwamandojin kungiyar 6.
Ana zargin Ikonson Commander, wanda shi ne kwamandan mayakan kungiyar ta IPOB, da cewa shi ne ya kitsa, tare da jagorantar kai farmaki ga shelkwatar ‘yan sanda ta jihar Imo, da kuma gidan yarin Owerri, da ma wasu hare-hare da dama a jihar ta Imo a ‘yan kwanan nan.
To sai dai a wata hira ta wayar tarho da gidan talabijin na CHANNELS, jami’in watsa labarai na kungiyar ta IPOB, Emmanuel Powerful, ya ce tuni da aka nada sabon kwamanda da zai maye gurbin Ikonson Commander.
“Ba zan fadi sunansa ba ko an tambaye ni, amma dai mun yi sabon kwamanda kuma muna nan daram,” in ji Powerful.
Karin bayani akan: DSS, Biafra, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Mai Magana da yawun kungiyar ta IPOB ya yi zargin cewa an kashe kwamandan na su ne saboda ya ki karba tayin shugabancin rundunar tsaro ta Ebubeagu da yankin da gwamnonin jihohin kudu maso gabas suka kafa.
Haka kuma ya zargi gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da kitsa farmakin da ya yi sanadiyyar hallaka Ikonson.
Marigayi Ikonson Commander, shi ne mutum na biyu a shugabancin kungiyar ta fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB, bayan babban jagoranta Nnamdi Kanu, wanda yazu haka ya arce daga Najeriya, a yayin da ake gudanar da shari'a tsakaninsa da gwamnatin tarayya a gaban kotu.
An zargi kungiyar ta IPOB da kaddamar da wasu sababbin hare-hare a jihar Imo da ma wasu makwabtan jihohi a yankin kudu maso gabas a 'yan kwanan nan, lamarin da ya ja hankalin jami'an tsaro, suka dauki matakin dakile hare-haren.
To sai dai kuma masu lura da al'amura sun yi hasashen cewa harin da aka kai wa gwamnan jihar a gidansa a jiya Lahadi, tamkar wata ramuwar gayya ce da kungiyar ta IPOB ta shirya, bayan zargin gwamnan da hannu a kisan kwamandanta.
An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi