Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan bindiga Sun Sake Kashe Biyu Daga Cikin Daliban Jami’ar Greenfield A Kaduna


Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

A ranar Talata maharan suka afka cikin jami’ar ta Greenfield mai zaman kanta wacce ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, suka yi awon gaba da dalibai da dama.

An sake gano karin wasu gawarwaki biyu daga cikin daliban jami’ar Greenfield da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, gwamnatin jihar Kaduna ta ce.

A ranar Juma’a ‘yan bindigar suka kashe uku daga cikin daliban jami’ar – hakan kuma na nufin adadin daliban da aka kashe daga makarantar ta Greenfield ya kai biyar kenan.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Kaduna, ta ce jami’an tsaro sun sake gano wasu gawarwaki biyu, kuma an kai su dakin ajiye gawa.

Gidan talbijin na Channels, ya ruwaito Kwamishinan tsaron cikin gida a jihar ta Kaduna, Samuel Aruwan yana tabbatar da aukuwar lamarin.

Karin bayani akan: ​Nasir El-Rufai, Atiku Abubakar, Shugaba Muhammadu Buhari, Kaduna, Nigeria, da Najeriya

A ranar Talata maharan suka afka cikin jami’ar ta Greenfield mai zaman kanta wacce ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, suka yi awon gaba da dalibai da dama.

Sun kuma kashe mai gadin makarantar a lokacin harin.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun nemi a biya su naira miliya 800 a matsayin kudin fansar daliban, wadanda har yanzu ba a san takamaiman adadinsu ba.

Wasu iyaye sun fadawa jaridar Daily Trust cewa, ‘yan bindigar sun yi barazanar za su rika kashe dalibai biyu ko sama da haka a kowane kwana uku idan ba a biya su ba.

A ranar Asabar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe dalibai uku na farko.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya tsaya takara da Buhari a 2019, ya nuna takaicinsa bisa kisan daliban.

“Jin labarin kisan 3 daga cikin daliban da aka sace a Jami’ar Greenfield a Kaduna, babban abin takaici ne.” In ji Atiku.

Matsalar satar mutane domin neman kudin fansa ta zama ruwan dare a arewa maso yammacin Najeriya.

A kwanakin baya, Gwamna Malam Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna, ya ce gwamnatinsa ba ta da shirin yin sulhu da ‘yan bindiga kuma ba za ta biya kudin fansa don sako mutane ba.

Har yanzu matsayar da gwammatin jihar Kaduna ta dauka yana nan daram. Gwamnati ba za ta tattauna ko ta biya ‘yan bindiga masu neman kudin fansa ba.” Hukumomin jihar suka fada a shafin Twitter.

Wasu daga cikin jihohin da wannan matsala ta addaba, sun yi yunkurin yin sulhu da ‘yan bindigar amma abin ya cutura.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG