Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TSARO: Shugaba Buhari Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Blinken


Sakataren harkokin wajen Amurka Tony Blinken ya gana ta yanar gizo da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Sakataren harkokin wajen Amurka Tony Blinken ya gana ta yanar gizo da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana gana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, inda suka tattauna kan batutuwan da suka hada da karfafa dangantakar kasashen biyu da kuma batun tsaro.

Wannan ganawa na wakana ne, a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro daga kungiyoyin ISWAP da Boko Haram yayin da matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa ta zama ruwan dare.

Wannan kuwa na zuwa ne albarkacin wani rangadi na farko ta na’urar sadarwar bidiyo da sakataren na harkokin wajen Amurka zai soma a yau, a kasashen Najeriya da Kenya na nahiyar Afirka.

Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka
Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka

Price ya ce a lokacin ziyarar ta na’ura, Antony Blinkin zai yi taro da shugaba Muhammadu Buhari, da kuma Ministan Harkokin Wajen Najeriyar Geoffrey Onyeama, domin sake karfafa matsayin dangantakar diflomasiyya tsakanin Amurka da Najeriya, wadda kuma ke da matukar muhimmanci ga dukan kasashen biyu.

Karin bayani akan: Antony Blinkin, Biafra, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

To sai dai ‘yan Najeriya da dama na fatar wannan ganawar za ta yi tasiri a sha’anin yaki da matsalar tsaro, da yanzu haka take kara habaka a dukkan sassan kasar.

Rahotanni na baya-bayan nan na nuni da cewa yanzu haka kungiyar Boko Haram ta karbe ikon a wata karamar hukumar mulki a yankin Arewa maso Gabas, da kananan hukumomin mulkin Kaure da Shiroro a jihar Naija da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Haka kuma ‘yan bindiga a wasu sassan Arewa maso Yamma na ci gaba da kai hare-hare inda suka ta da garuruwa da dama, kazalika da uwa-uba, satar mutane domin karbar kudin fansa.

A yankin kudancin kasar ma kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biafra, ta sabunta kai hare-hare biyo bayan kashe kwamandanta a karshen mako, inda a baya-bayan nan ma suka kai farmaki a wani gidan Fulani, suka yi wa mutane 19 kisan gilla a jihar Anambra.

XS
SM
MD
LG