A yau Lahadi, kafofin yada labarai a Korea ta Kudu, sun ruwaito cewa, wani babban jami’in kasar Korea ta Arewa ya kama hanyarsa ta zuwa kasar Findland domin haduwa da wasu tsoffin jami’an diplomasiyyar Amurka.
Hakan na faruwa ne, bayan da wata tawagar jami’an Korea ta Arewa suka kammala wata tattaunawa ta kwanaki uku, da jam’ian diflomasiyyar kasar Sweden.
Wannan tattawaunawa ana ganin ita za ta share fagen ganawar shugaba Donald Trump da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, Kim Jong Un.
Kamfanin dillancin labaran Yonhap na Korea ta Kudu, ya ruwaito cewa an ga mataimakin shugaban da ke kula da hulda tsakaninn Korea ta Arewa da yankin arewacin Amurka, Choe Kang II, a filin tashin jirage na kasa da kasa, da ke Beijing.
Daga baya anga ya shiga jirgi ya kama hanyarsa ta zuwa Findland.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa tsohuwar Jakadiyar Amurka a Korea ta Kudu, Kathleen Stephen, na daya daga cikin tsoffin jami’an diflomasiyan Amurka da za su gana da jami’in na Korea ta Arewa a kasar ta Findland.