Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wane Ne Mike Pompeo?


Zabin shugaba Trump kan mukamin sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo
Zabin shugaba Trump kan mukamin sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo

Michael Richard Pompeo, wanda aka fi sani da Mike Pompeo, shi ne mutumin da shugaban Amurka Donald Trump ya zaba ya maye gurbin Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson da aka kora. Karanta kadan daga cikin tarihinsa.

Bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sallami tsohon Sakataren harkokin wajen kasar, Rex Tillerson daga mukaminsa, ya nada shugaban hukumar leken asirin kasar ta CIA, Mike Pompeo.

Ga wadanda ke bibiyar siyasar Amurka, Pompeo ba bakon suna ba ne a sha’anin gudanarwa a Amurka, domin an jima ana damawa da shi.

Pompeo ya taba yin wa’adi uku a majalisar dokokin Amurka a karkashin jam’iyar Republican inda ya wakilci jiharsa ta Kansas.

Ya na daya daga cikin mutanen da suka fara marawa shugaba Trump baya a lokacin da ayyana shirinsa na tsayawa takarar shugabancin Amurka.

A lokacin da yake majalisa, ya kasance daya daga cikin jagororin da ke sukar shirin kiwon lafiya nan mai rahusa na Obamacare.

Ya kuma ki jinin yarjejeniyar nukiliya nan da aka kulla tsakanin Amurka da wasu manyan kasashe biyar a gefe daya da kuma Iran a gefe guda a 2015.

Bayan da shugaba Trump ya bayyana cewa ya amince a tattauna da Korea ta Arewa, cikin hanzari Pompeo ya mara masa baya.

“Ba mu taba samun dama irin wannan ba, inda Korea ta Arewa wacce tattalin arzikinta ke fuskantar matsi, har ta kai ga shugabaninsu suka fara tunanin tattaunawa.” Inji Pompeo.

Idan har majalisar ta amince da zabinsa, Pompeo zai zama mutum na farko da ya shugabanci hukumar leken asirin kasar ya kuma zama sakataren harkokin wajen Amurka.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, shugaban kwamitin da ke kula da harkokin wajen Amurka a majalisar Dattawa, Bob Corker, ya ce ana sa ran a watan Afrilu za a yi zaman tantance kwarewar Pompeo.

Daga cikin kalubalen da masana harkar dipflomasiyya suka bayyana Pompeo zai tunkara idan an tabbatar mai da mukaminsa, akwai batun tattaunawa da Korea ta Arewa da kuma yarjejeniyar nukiliyan Iran.

Amma wani rauni da suke ganin Pompeo yake da shi, shi ne, ba shi da kwarewar harkokin diflomasiyya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG