A ganawar tasu, wakilin Amurka Robert Lightizer da kwamishinan cinikayya ta Tarayyar Turai Cecilia Malmstrom da takwararsu na kasar Japan Hiroshige Seko sun tattauna a kan yanda bangarorin zasu yiwa juna adalci a huskar kasuwanci.
Tarayyar Turai ta fada a wata sanarwa cewa ita da Japan suna da matukar damuwa a kan wannan kudin fito na Amurka. Manyan kasashen masu tasiri, kuma manyan abokan kasuwancin Amurka sun bukaci a fiddasu daga wannan kudin fiton.
Jim kadan bayan tattauanawar, Malmstrom, ta dora a kan shafinta na Tweeter cewar babu alama ko Amurka zata fiddasu a cikin batun harajin, don haka tattaunawa zata ci gaba a mako mai zuwa.
Shiko Seko mai wakiltan Japan, ya fada a wani taron manema labara bayan ganawar, yace yayi tsayin daka kuma ya bayyana matsayinsa cewa wannan batu abin takaici ne, ya kuma ce wannan abu zai yi mummunar tasiri a kan bakin dayan tsarin huldan cinikayya.
Facebook Forum