Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kan Shirye Shiryen Ganawar Trump Da Kim Jong-un


Ministan Harkokin Wajen Koriya Ta Arewa
Ministan Harkokin Wajen Koriya Ta Arewa

Ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa Ri Yong Ho ya nufi Sweden a balaguron da ake jin zai share fagen yiwuwar a yi taron koli tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jon Un.

Yau Alhamis ake sa ran Ri, zai isa Stockholm, inda zai kwashe kwanaki biyu yana tattaunawa da takwarar aikin sa ta Sweden Margot Wallstrom. Sweden na wakiltar muradun Amurka ta diflomasiyya, da Canada da Austarlia a ofishin jakadancin kasar dake Koriya ta Arewa.

Ma'aikatar harkokin wajen Sweden tace ziyarar Ri "zata bada gudummuwar" tabbatar da an ai watar da kudurin kwamitin sulhu na Majalisa Dinkin Duniya, wadda tayi Allah wadai da hukumomin Pyonyang, kan shirin nukiliya da kuma makamai masu linzami na kasar.

Shugaba Trump ya bada sanarwar bazata a satin da ya gabata inda yace zai gana da shugaba Kim Jong Un a karshen watan Mayu, amma ba'a bada sanarwar wuri da kuma ranar da za'a yi taron kolin ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG