Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukuntan Amurka Ba Za Su Yi wa Koriya ta Arewa Wani Sassauci Ba


 Mike Pompeo daraktan hukumar leken asiri ta CIA
Mike Pompeo daraktan hukumar leken asiri ta CIA

Daraktan hukumar CIA ta Amurka ya ce za'a ci gaba da yi wa Koriya ta Arewa matsin lamba har zuwa lokacin taron kolin da ake kyautata zaton shugaban Amurka da na Koriyan zasu yi a watan Mayu.

Mahukunta na Amurka sun lashi takobi jiya Lahadi cewa babu wani sassaucin da za ayi wa Koriya ta Arewa kafin taron kolin da ake sa ran yi tsakanin shugba Donald Trump na Amurka da shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa, maimako ma za aci gaba da matsa mata lamba ne.

Darektan hukumar leken asirin Amurka ta CIA, Mike Pompeo, ya fadawa shirin telebijin na Fox News Sunday a jiya lahadi cewa, "Babu wani sassaucin da za a yi ma Koriya ta Arewa a yayin da ake wannan tattaunawa."

Pompeo yace tilas ne shugaban na Koriya ta Arewa "ya bar mu muci gaba da gudanar da ayyukan da sojojinmu suke bukata tare da Koriya ta Kudu, sannan ya tabbatar da cewa za a iya tattaunawa a kan batun raba sojojinsa da makaman nukiliya."

Mai Magana da yawun fadar White House, Raj Shah, ya fadawa gidan talabijin na ABC cewa shugaba Trump "ya ki rungumar manufofin da suka kasa aiki a shekarun baya, watau yadda Amurka ke nuna sassauci a lokacin tattaunawa kafin a cimma komai." Yace, "manufarmu ita ce matsin lamba. Matsin lamba daga kawayenmu a fadin duniya, matsin lamba daga MDD da kuma matsin lamba daga kasar China."

Yace kara da cewa, wadannan matakan sun sauya ma shugaba Kim Jong Un tunani da dabi'a, kuma su na fata irin wannan matsin lamba, wanda ba za a sassauto da shi ba, zai sa kasar Koriya ta Arewa ta sauya dabi'unta.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG