Babban kamfanin hada magunguna na Amurka, Johnson & Johnson, ya fara gwaji na karshe na allurar rigakafin cutar COVID-19 a jikin mutane a Amurka.
Babban jami’in kimiyya a kamfanin na Johnson & Johnson, Dr. Paul Stoffels, ya shedawa manema labarai jiya Laraba cewa, mutane dubu 60,000 suka shiga cikin shirin da suka fara karbar allurar rigakafin a sassa 215 da ke Amurka, kazalika da kasashen da suka hada da Argentina, Brazil, Chile, Colombia, Mexico, Peru da kuma Afirka ta Kudu.
Dr. Stoffels ya ce Johnson & Johnson ya shiga gwajin a mataki na karshe ne, bayan da aka ga alamun nasara a gwaje-gwajen da aka yi a mataki na 1 da na 2 a Amurka da Belgium.
Allurar rigakafin Johnson & Johnson ita ce ta hudu cikin aluran rigakafin coronavirus da ake kyautata zaton za su yi aiki, wadanda ake kuma gwajinsu a mataki na uku a Amurka, baya ga na kamfanin Moderna, AstraZeneca da kuma wani gwajin hadin gwiwa da kamfanonin Pfizer da BioNTech na Jamus suke yi.
Dukkan wadannan yunkuri hudu da ake yi, na gudana ne karkashin kulawar wani shirin gwamnatin Trump na samar da rigakafin cutar ta coronavirus da ake kira “Operation Warp Speed coronavirus vaccine initiative,” wanda yake da burin samar da rigakafi guda miliyan 300 da za a amince da ita nan da zuwa watan Janairun 2021.