Yayin da Yawan wadanda cutar corona ta kashe a Amurka ya doshi 200,000, babbar cibiyar lafiyar kasar ta gaggauta cire wani bayanin da ta saka a shafinta na internet, kan yadda cutar ke yaduwa.
Cibiyar yaki da cututtuka masu Yaduwa ta Amurka (CDC), ta wallafa wani bayani a ranar Jumma’ar da ta gabata mai nuna cewa, cutar corona na iya yaduwa ta kurar da ke bin iska, wadda ake kira aerosols, a tazara mai dan yawa.
To amma kwatsam sai cibiyar ta cire wannan bayanin ranar Litini, ta koma kan matsayinta na farko na cewa, cutar corona na yaduwa ne akasari tsakanin mutanen da su ka tsaya da tazarar mita 1.8, da kuma tururi da yawun da kan fito yayin magana, tari ko atishawa.
Dr. Jay Butler, Mataimakin cibiyar ta yaki da cututtuka masu yaduwa, ya ce an wallafa bayanin na baya baya ne cikin kuskure gabanin tantance shi yadda ya kamata.
An dai sha yin zazzafar takaddama tsakanin kwararru kan yadda COVID-19 ke yaduwa. A watan Janairu, masu ilimin kimiyya sama da 200 daga kasashe sama da 30, sun buga wata budaddiyar wasika zuwa ga Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), ta kiran hukumar da ta yi nazarin hujjojin da ke nuna cewa, cutar corona na iya yaduwa ta iska.
Facebook Forum