Batu da yafi daukar hankali a jawaban shugabannin manyan kasashen duniya a jiya Talata, shine lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya kara kiran cutar coronavirus da “China Virus” wato kwayar cutar China. A cikin jawabin sa shugaban na Amurka ya Ambato nasarori da Amurka ta samu a yaki da wannan cutar COVID-19.
Shugaba Trump ya nanata batun da ya saba fadi na tilastawa China ta yiwa duniya bayani game da wannan cutar. Ya ce dole ne mu tuhumi kasar China da ta saki wannan cuta, ya ce a farkon bullar cutar China ta hana tashin jirage a cikin kasar ta amma ta ba jiragen kasa da kasa daman jigilar fasinjoji domin baza cutar a duniya.
Jawaban da shugabannin duniya suka yi ta yanar gizo sakamakon cutar COVID-19, sun mai da hankali ne a kan yaki da cutar wanda hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO ke jagoranta. Taron Majalisar Dinkin Duniya na cikon shekaru 75 ya gudana ne a cikin wani yanayi da ba a taba gani ba.
Shugaban kasar China Xi Jinping ya ce kasar China bata da niyar shiga yakin cacar baki ko wani yaki na daban da wata kasa kana China zata ci gaba da bada gudunmuwarta ga yaki da cutar da ta yiwa duniya lahani. Xi ya yi kira ga kasashen duniya da a yi watsi da duk wani yunkuri na saka siyasa a wannan yaki da cutar, ya ce tinkarar wannan cuta na bukatar tabbatar da kwararan matakai na tsawon lokaci.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na cikin wadanda suka yi jawabi a jiya Talata, inda ya ambato yadda Najeriya take tinkarar yaki da cutar coronavirus. Shugaban ya ce Najeriya ta ciyo nasarori da dama amma akwai bukatar aikin hadin gwiwa tsakanin kasashe a wannan yaki da cutar.
Shugaban na Najeriya ya tabo batun tsaro inda yake cewa “Najeriya na matukar bakin cikin a kan yanda ake safara da raba kananan makamai da kuma baza su musammanan a nahiyar Afrika.”
Shugaba Buhari ya ce Najeriya zata ci gaba da aiki da sauran kasashen duniya wurin yaki da talauci da ta’addanci da kuma samar da ci gaba musamman a kasashe masu tasowa. Sai dai ya jaddada kira da ya saba yi na baiwa Afrika kujera ta dindindin a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.
Saurari rahoton da Sarfilu Hashim Gumel ya shirya mana:
Facebook Forum