Cututtukan na murar da coronavirus na da saurin yaduwa kuma suna da alamu iri daya.
Banbancin shi ne, ita cutar murar na zuwa ne lokaci-lokaci, yayin da ita kuma ta COVID-19 ba ta da lokaci take kuma ci gaba da yaduwa a sassan duniya.
Duk da cewa har yanzu ba a samu rigakafin cutar ta coronavirus ba, an kwashe gomman shekaru ana amfani da rigakafin cutar ta mura.
Kwararru a fannin lafiya sun ce hanya daya da za a iya sanin ko mutum na dauke da daya daga cikin wadannan cututtuka ita ce – ta hanyar yin gwaji.
Darekta a sashen bincike kan cututtuka masu yaduwa a jami’ar George Washington, Gary Simon, ya fadawa jaridar Washington Post cewa, yiwuwar samun damar shawo kan wadannan cututtuka biyu, ya sa shekarar nan ta 2020 ta zama “mai matukar wuya.
Izuwa yau Asabar, Sashen kula da cutar ta coronavirus a Jami’ar Johns Hopkins ya ce akwai mutum miliyan 30.5 da ke dauke da cutar a duniya, sannan ta yi sanadin mutuwar kusan mutum miliyan daya.
Facebook Forum