An Yi Kira a Yi Adalci ma Kowani Dan Kasa Tun Kafin Gudanar da Zaben Najeriya

  • Ibrahim Garba

Wani dan Nijeriya na nuna katin zabe na dindindin.

An yi kiran da a yi adalci ga kowani dan Nijeriya da ya rasa waninsa ko dikiya a tashe-tashen hankulan kasar saboda a rage dumamar zamantakewa kafin zabe.

Rikice-rikicen ‘yan tsagerun Naija-Delta da na kabilanci da addini a yankin tsakiyar Nijeriya da kuma na Boko Haram, musamman ma a arewacin Nijeria sun kusa durkuzar da Nijeriya, don haka ya kamata ‘yan takarar Shugabancin Nijeriya su bayyana yadda za su magance wadannan matsalolin. Hasashe kenan da kuma shawarar Shugaban Rundunar Adalci, Abdulkarin Dayyabu.

Da ya ke amsa tambayar wakilinmu a Abuja Nasiru Adamu Elhekaya, Malam Dayyabu ya, “Magana ce ta cewa sai an zo an yi garanbawul, a ‘total reshuffle,’ a yi ‘total redemption,’ a kwato wa kowa hakkinsa; a kafa Raddil Mizalim a kwato wa kowa hakkinsa a danka masa a hannu.” Ya ce duk wanda aka kashe masa uba ko da ko dan’uwa ko mata ko miji a biya shi diyya. Ya ce muddun ba haka aka yi, to yaudarar kai kawai ake yi.

To amma ‘yan siyasa na cigaba da nesanta kansu daga duk wata barazana ga zaben da ke tafe, tare da alkawarin magance wadannan matsalolin. Babban Sakataren Jam’iyyar adawa ta APC, Mai Mala Boni ya ce duk jam’iyyar PDP ce ke ta kiraye-kirayen a jingirta zabe saboda sun firgita bayan ko gudanar da zaben shi ya fi fa’ida. Shi kuwa tsohon shugban PDP Alhaji Bello Halliru ya ce ya dace PDP ta cigaba da mulki saboda kwarewarta.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN NIJERIYA