Mayan jam’iyun siyasa, a Najeriya, PDP da APC, sunyi na’am da salon gudanar da yakin zabe, wanda babu zage-zage da kuma batanci, a fafutukar yakin neman kuri’ar, jama’ar kasa da aka kulla a tsakanin shugaba Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari.
Jam’iyun sun nemi ganin yarjejeniyar da aka kulla a matakin tarayya, an aiwatar dashi a jihohi, domin tsarkake siyasar gaba da kuma fadace-fadace a tsakanin magoya bayan jam’iyun.
Muhammadu Inuwa Yahaya, dan takarar kujerar Gwamna, a karkashen jam’iyyar, APC, ya bukaci ganin cewa an shinfida wannan tsari a jihar Gombe.
Yana mai cewa “Ai abunda duk zai kawo zaman lafiya, a matsayin mu na masu hankoron shugabanci shi yakamata muso ba wanda zai kawo tashin hankali ba, inda ana zama na gaskiya, ai da aka yi tsarin nan daga Abuja, yakamata a aikawa kowace jihar, tunda Najeriya, ai guda daya ce.”
Daraktan janar, na yakin neman zabe a jam’iyyar PDP, a jihar Gombe, Sanata Umar Kumo Garkuwan Gombe, yace siyasa a cikin kwanciyar hankali shine abunda suke fatar ganin an aiwatar a jihar Gombe.
Yace” Wallahi mun fi kowa son a zauna lafiya, domin kullum wanda ke rike da abu shi yafi so a zauna lafiya, kuma muke rike da Gwamnatin jihar Gombe, saboda haka muke da bukatar zaman lafiya, mune ma muke cewa kada ayi siyasa, ta fadace-fadace, domin mu muke bukatar jama’a, kuma jama’ar nan su zamu mulka.”